pep.zone
Welcome, guest. You are not logged in.
Log in or join for free!
 
Stay logged in
Forgot login details?

Login
Stay logged in

For free!
Get started!

Mobile Blog


dadylasting.pep.zone

LIFE STORY

03.11.2014 15:54 EST
LIFE STORY
zaune nake a majalisa nayi shiru nayi takumi ina tunanin duniya.
Dayake yau litinin ce ranan cin kasuwar garin muce.
Duk abokanaina sun tafi dako kasuwa.
Nima din bandade da dawowa ba.
Amma saide yau gaskiya ba'a dace ba dan tun safe nake zagaya kasuwa amma ko mutum daya ban daukarwa dakoba.
Ni kadaine a zaune a majalisar nayi shiru ina tunanin yanayin rayuwa kawai sainaji cikina ya murda alamun yunwa nakeji. Sainayi niyar tashi naje gida danko kanzo ne abani inci.
Tun kafin na karasa gida najiwo ihun kaka ta. Nantake gabana yafadi saboda nasan cewa inde tana masifa ba'abinda zan samu a gida hakan yasa nakoma baya zuwa majalisa saboda nasan ma innaje gida rainane zai baci.......
Ni D...LASTING nazauna nayi shiru a majalisa kawai sainaji horn din wata mota ina daga kaina sainaga wata sabuwar mota ce kirar [BMW X5] kallo 1 nayiwa motan na kauda kai saboda nasan cewa kallon motan bakin ciki zai karamin.
Kawai sainaga motan ta tsaya a daidai inda nake.
Ni ko daga kaina banyiba waidan naga waye a cikin motan. [ashe wata zukekiyar budurwa ce a cikin motan]
yarinyar dake cikin motan tafito tamin sallah na amsa aciki ciki.
Tace dan allah malam ina tambaya.
Nace allah yasa nasani.
Tace kokasan wani gaye waishi D...LASTING.
Sainayi jin nace shigayen koyayi maki wani laifine?
Tace a'a kawai de ina neman sane domin inaso na kulla wata halaka dashi.
Nace da ita hmm eh nasan dadylasting amma zanso naji wani irin halaka kikeso ki kullah dashi.
Tacemin stop here. Banzo wajenka muyi hira ba. Inzaka gayamin inda yake to.
Hmm nan nayi karfin hali nace da'ita nine dadylasting.
Tamin wani kallo me cike da alamun rashin yarda.
Tayi dariya me dadin sauraron me sauraro haryasa nadena jin yunwan danakeji
tace dani inda kace kaine dadylasting zamma wasu tambayoyi guda uku. Inde ka amsamin zan tabbar cewa kaine.
Amma yanzu kazo muje mushiga cikin mota dan wajen akwai zafi. Sainama tambayoyin
nannayi karfin halinace da ita ranki dade a gsky bazan iya shiga cikin motar kiba domin cewa ni bandamu na kulla halaka dake ba saboda nasan cewa xxx sainayi shiru.
Tace da muryarta me dadin sauraro [inda zan shekara inajin sautin muryarta bazan gaji ba]
meyasa baka karasa nace bakomai.
Tacemin tana zuwa tana shiga cikin motan tafito da wani abu kallo 1 nayiwa abun numfashi na ya dauke.
Hmmmmmm


This page:
Help/FAQ | Terms | Imprint
Home People Pictures Videos Sites Blogs Chat
Top
.