pep.zone
Welcome, guest. You are not logged in.
Log in or join for free!
 
Stay logged in
Forgot login details?

Login
Stay logged in

For free!
Get started!

Mobile Blog


dadylasting.pep.zone
07.11.2014 01:10 EST
BINCIKEN DA ZAUREN FIQHU YA GUDANAR, YA GANO CEWA AKWAI NAU'IKAN SHAITANUN ALJANU KALA GOMA SHA HUDU (14) WADANDA SUKE SHIGA JIKIN 'YAN ADAM, KAMAR HAKA :
1. JINNUL ASHIQ - Aljanin Soyayya. Wanda yake shiga 'yar Adam (mace) budurwa ko matar aure ya hanata Samun aure. Ko kuma ya raba auren in akwai shi.
2. JINNIYYATUL AASHIQAH: aljanar soyayya wacce take shiga jikin Dan Adam namiji, har ta hanashi aure. kuma tana zuwa masa amafarki tana saduwa dashi.
3. JINNUL GAWWAS - Aljanin Ruwa. irin wannan aljanin idan yana jikin mutum, zai rika yawan shan ruwa, yawan mafarkin ruwa, yawan wanka, ko dadewa sosai acikin ruwa.
4. JINNUT TAYYAR - Aljani mai fuka-fukai mai tashi kamar tsuntsu. irin wannan shaitanin Aljanin yana da mutukar yaudara, da kuma wuyar sarrafuwa agun masu rukiyyah. kuma sune aljanu mafiya dadewa adoron Qasa.
5. KHADIMUL HAMMAM - Aljanin bandaki (Sarkin Qazamai). shine wanda idan yana jikin mutum zaka ganshi kusan ko yaushe acikin Qazanta da dattin jiki da dattin sutura. Kuma zaka ga mutumin yana yawan dadewa sosai acikin bandaki duk lokacin da ya shiga.. Kuma duk inda ya shiga ba zaiji kwanciyar hankali ba, sai dai in ya shiga bandaki.
6. JINNUL MAQABIR - Aljanin Makabarta, ko kuma Fatalwa. Shi irin wannan aljanin idan yana jikin Dan Adam, to mutumin zai yawaita mafarkin Matattu, ko kuma Mafarkin shiga Makabarta, ko kuma wani lokacin atsinci mutum acikin Makabartar..
7. 'AMIRUL BAITI - Aljanin gida. ('Dan Gwai-gwai). Irin wannan Aljanin yana zaune ne tare da mutane acikin gidajensu, kumq yafi kowanne Aljani sanin yanayin zamantakewar Bil Adama.
Yakan ci abincin masu gidan idan sun dafa ba tare da ambaton sunan Allah ba.
8. JINNUL JALBI WAT-TAHDHEER - Aljanin da matsafa suke amfani dashi domin satar kudaden Mutane, ko kuma daukar abu daga wani wajen zuwa wani wajen..
9. JINNUL ATFAL - Jinjirin Aljanu, shine wanda yake shiga jikin Qananan yara. Yana da mugunta sosai. Kuma yakan rika tsoratar da yara, yana razanasu, yana sanya yaro ya rika tsalla kuka da tsakar dare.
Wani lokacin kuma yakan dakile jikin yaro ya hanashi girma, ya hanashi kuzari.
10. JINNUL LAMSAH : Aljani mai shanye jikin 'Dan Adam. Yanayinsa yafi kama da Aljanin ruwa.
11. JINNUT TABADDUL - Aljanin da yakan dawo yaro bayan ya Tsufa. Akan samu musulmai da yawa acikinsu.
12.JINNUN FILOUSUFIY - Aljani mai ilimi wanda ya riga ya karanci halayyar 'yan Adam. Akwaishi da zance, da zakin baki. Kuma yana da yawan jayayya.
13. JINNUL KAMIL - Aljanin da yakan shiga jikin 'Dan Adam, yana cutar da Dan Adam sosai amma ba ya barin wata alama wacce za'a ganeshi. Kuma ko anyi rukiyya bai cika bayyana ba.
14. JINNUL QAREEN - Shine nau'in Aljanin nan wanda yake jikin kowa da kowa. Dukkan mutane suna dashi. Shine wanda kullum yake umurnin Dan Adam ya aikata miyagun ayyuka.
15. KHADIMUS SIHRI - Aljanin da yawancin bokaye da matsafa suke turoshi domin kashewa ko haukatar da 'Yan
Adam.
Yawancinsu kamar 'Yan Daba suke, akwaisu da shan jini. Da kuma mugunta sosai. Sannan suna da naci. Dole sai an samu Gwani aharkar Ilimin Rukyah sannnan ake cin galaba akansu.
Kowanne daga cikin wadannan yana da alamomin da muke ganeshi, da kuma bambanci tsakaninsa da waninsa.
Kuma kowanne daga cikinsu akwai irin ayoyin da suka fi Konashi. Kuma akwai irin nau'in Maganin da yafi tasiri akansa.
Insha Allahu nan gaba zamuyi bayani
dalla-dalla


This page:
Help/FAQ | Terms | Imprint
Home People Pictures Videos Sites Blogs Chat
Top
.