pep.zone
Welcome, guest. You are not logged in.
Log in or join for free!
 
Stay logged in
Forgot login details?

Login
Stay logged in

For free!
Get started!

Mobile Blog


dadylasting.pep.zone

nayi zurfin ciki

03.12.2014 01:58 EST
****ZURFIN CIKI*****
SHEKARANMU TA FARKO A JAMI'A
A cikin ajin turanci (english), ina zauna kusa da
ita, tana kirana da babban amininta. Niko
batasan ba hakan nake so ba, ina fata ta zama
tawa, amma bata gane ba kuma nasan hakan.
Bayan angama darasi ta tambayeni note din da
akayi jiya da bata xoba, ni kuma na bata,
takalleni tai mun wani tattausan murmushi tace
" na gode" Naso in gaya mata ina santa
amma na kasa saboda kunya kuma na rasa
gane dalilin hakan.
SHEKARA TA BIYU
=================
wayan ta yayi ringing bayan ta dauka ta gama
maganan da zatayi a wayan sai naga idanunta
sun ciko da kwallah da alamun damuwa a tare
da ita. Tana shashshekan kuka tace dani
"don A llah zo ka tayani hira domin
bansan nazauna ni kadai kasan cewar nina
cikin damuwa, nazauna kusa da ita ina kallon
kwayar idonta, ina fata araina tazama tawa
bayan munsami kamar awa biyu sai tacemun
"nagode " ta sakarmun da wani tattausan
murmushi. Inaso in fadamata ina santa nikuma
nakasa saboda kunya. Bansan dalilin hakan ba.
RANAN GAMA MAKARANTA
====================
Kwanaki na wucewa, satututtuka, haka watanni,
kafin in farga har ranan gama makaranta tayi.
Na kalli kyakykyawar halittar da Allah ya mata ,
naso ta zama tawa bata gane ba kuma nasan
hakan.
Kafin kowa ya watse yaje gida tazo guna idonta
cike da kwalla da alamun damuwa atare da ita.
Ta rungumeni saannan tasa hannunta a
kafaduna tace "kai ne babban amini na nagode
da kulawarka a gareni na tsawon zaman da
mukayi" Naso infada mata ina santa amma na
kasa fada, banso inzama babban amininta
kadai, inaso inzama masoyinta ne, amma
nakasa fadamata inajin kunya. ita bata ganeba,
nima nasan hakan.
Bayan wasu shekaru
==========
Ina zaune sai naga takardan gayyata zuwa
wajen bikinta. Nayi bakin ciki kamar bazanje ba
amma sai nai ta maza na daure naje..
Tayi matukar farin cikin ganina tace "wannan
shine ‪#‎ Musty‬babban amini na a makaranta, ya
kula dani sosai," Nakuma gode da karamcinka
amini na. Ni kuwa ina santa ne amma na kasa
fadamata saboda kunya ita bata ganeba.
======
watarana daga cikin ranakun da nake zaune ina
tinanin wacce nima nace wa "babban aminiyata
" inaso naga fuskarta , kawai sai na tina da
album dimmu nagama makaranta da mukayi ,
kasancewar tin da muka gama makarantas ban
duba ba sai yau , shima dan akwai dalili ne..
Ga abin da nagani awajen hoton wacce nake
cema aminiyata,
bayan suna da adireshi nata da ranan haihuwa .
Sai kuma inda aka rubuta mutum ya rubuta
abinda bazai taba mantawa dashiba a rayuwar
makarantan shi, ga abinda naga ta rubuta
KULLUM INA ZAUNE KUSA DA SHI, NAYI FATAN
YAZAMA NAWA, AMMA BAI GANE BA, KUMA NA
FAHIMCI HAKA, NASO ACE YA GANE, BAWAI
INASO YAZAMA AMININA KADAI BANE, INA
SANSHI AMMA INAJIN KUNYA, KUMA BANSAN
MEYASA HAKAN BA, NASO ACE YA FADAMUN
YANA SONA, NIMA NASO INFADA MASA, NAYI
KOKARIN HAKAN, AMMA KUNYA TA HANANI ,
NAI KUKA NAI BAQIN CIKI.
DARASI: Idan kana ko kina san wani ku
gaggauta sanar da juna domin kar kuyi
danasani daga baya..
ZURFIN CIKI BAIDA AMFANI A SOYAYYA


This page:
Help/FAQ | Terms | Imprint
Home People Pictures Videos Sites Blogs Chat
Top
.