pep.zone
Welcome, guest. You are not logged in.
Log in or join for free!
 
Stay logged in
Forgot login details?

Login
Stay logged in

For free!
Get started!

Mobile Blog


dadylasting.pep.zone
24.06.2015 15:28 EDT
RAMADAN MUVARAK!! Via daily hadith Abu Huraira (RA) yace: Manzon Allah s.a.w yace, “Duk wanda yake azumi kuma ya kasa barin yin karya da aikata miyagun ayyuka maras kyau, to ya sani cewa hakika Allah baya da bukata daga barin cin abincinsa da kuma abin shansa ma'ana Allah baya da bukata da azuminsa.” Hadisin: Sahih Bukhari 1804. ‪# ARABIC_TRANSLAT ION‬ ﻋﻦﺃﺑﻲ ﻫﺮﻳﺮﺓﺭﺿﻰ ﺍﻟﻠﻪ ﻋﻨﻪ ﻗﺎﻝﻗﺎﻝﺭﺳﻮﻝﺍﻟﻠﻪﺻﻠﻰ ﺍﻟﻠﻪ ﻋﻠﻴﻪ ﻭﺳﻠﻢ ﻣﻦﻟﻢﻳﺪﻉﻗﻮﻝ ﺍﻟﺰﻭﺭﻭﺍﻟﻌﻤﻞﺑﻪﻓﻠﻴﺲﻟﻠﻪ ﺣﺎﺟﺔﻓﻲ ﺃﻥﻳﺪﻉﻃﻌﺎﻣﻪ ﻭﺷﺮﺍﺑﻪ Ya Allah ka hane mu daga fadar karya a koda yaushe. Ya Allah kasa mu kasance, daga cikin bayinka masu fadin gaskiya komai rintsi, komai wahala. Ya Allah ka hane mu, daga aikata miyagun ayyuka maras kyau. Ya Allah ka shiryar damu akan bin sunnar Annabin ka, Annabi Muhammad Sallahu Alaihi Wasallam ‪#Ameen admin dadylasting www.facebook.com/dadylasting
.
.
.
.
.
.
.
.
RAMADAN KAREEM..
‪#‎ HADITH‬
Abdullahi Ibn Mas’ud (RA) yace: Watarana na tambayi Manzon Allah s.a.w cewa, “Ya Rasulillah wane aiki ne mafi kyawo?” Manzon Allah s.a.w ya amsa da cewa, “Yin Sallah acikin lokacin ta.” Abdullahi Mas'ud yace sai na kara tambayar sa, “Bayan wannan kuma sai wane aiki?” Manzon Allah s.a.w ya amsa da cewa, “Yiwa Iyaye da'a tareda kyauta ta musu.” Abdullahi Mas'ud Yace sai na kara tambayar sa, “Bayan wannan kuma sai wane aiki?” Manzon Allah s.a.w ya amsa da cewa, “Yin Jahadi domin Allah” Abdullahi Mas'ud yace daga nan sai nayi shuru da bakina ban kara yi masa wata tambaya ba, saboda idan na cigaba da yi masa tambaya to kuwa ba zai taba gajiyawa ba zai cigaba da bani amsar duka tambayoyin nawa da yawa.
Hadisin: Sahih Bukhari
na 2630, da kuma Hadisin Sahih Muslim na 85.
‪#‎ ARABIC_TRANSLAT ION‬
ﻗﺎﻝﻋﺒﺪﺍﻟﻠﻪﺑﻦﻣﺴﻌﻮﺩﺭﺿﻲ
ﺍﻟﻠﻪﻋﻨﻪﺳﺄﻟﺖﺭﺳﻮﻝﺍﻟﻠﻪﺻﻠﻰ
ﺍﻟﻠﻪﻋﻠﻴﻪﻭﺳﻠﻢﻗﻠﺖﻳﺎ ﺭﺳﻮﻝ
ﺍﻟﻠﻪﺃﻱﺍﻟﻌﻤﻞﺃﻓﻀﻞﻗﺎﻝ
ﺍﻟﺼﻠﺎﺓﻋﻠﻰ ﻣﻴﻘﺎﺗﻬﺎ ﻗﻠﺖﺛﻢﺃﻱ
ﻗﺎﻝﺛﻢﺑﺮﺍﻟﻮﺍﻟﺪﻳﻦﻗﻠﺖﺛﻢﺃﻱ
ﻗﺎﻝﺍﻟﺠﻬﺎﺩﻓﻲ ﺳﺒﻴﻞﺍﻟﻠﻪ
ﻓﺴﻜﺖﻋﻦﺭﺳﻮﻝﺍﻟﻠﻪﺻﻠﻰ
ﺍﻟﻠﻪﻋﻠﻴﻪﻭﺳﻠﻢﻭﻟﻮﺍﺳﺘﺰﺩﺗﻪ
‪#‎ ALLAHU_AKBAR‬: 'Yan uwa kun jifa! Dan haka sai mu kara dagewa sosai wajen amfani da wadannan darussan da suke acikin wannan Hadisin, domin samun dacewa a wajen Rabbil-Izzati.
Ya ALLAH ka tausaya muna, ka sada mu da rahamar ka a duniya da lahira. Ya ALLAH kasa muna daga cikin yardaddun bayin ka, wadanda kake so kuma kayiwa Alqawarin gidan Aljannah a ranar gobe qiyawa dan Albarkacin dan Ameenah da Abdullahi Muhammadur-Rasulullahi Sallallahu Alaihi Wasallam
‪#Ameen
Admin
dadylasting
www.facebook.com/dadylating
.
.
.
.
.
.
.
.
AFTERNOON HADITH
RAMADAN MUVARAK!!!
Abu Huraira (RA) yace: Manzon Allah s.a.w yace, “Duk wanda yake azumi kuma ya kasa barin yin karya da aikata miyagun ayyuka maras kyau, to ya sani cewa hakika Allah baya da bukata daga barin cin abincinsa da kuma abin shansa ma'ana Allah baya da bukata da azuminsa.”
Hadisin: Sahih Bukhari
1804.
‪#‎ ARABIC_TRANSLAT ION‬
ﻋﻦﺃﺑﻲ ﻫﺮﻳﺮﺓﺭﺿﻰ ﺍﻟﻠﻪ ﻋﻨﻪ
ﻗﺎﻝﻗﺎﻝﺭﺳﻮﻝﺍﻟﻠﻪﺻﻠﻰ ﺍﻟﻠﻪ
ﻋﻠﻴﻪ ﻭﺳﻠﻢ ﻣﻦﻟﻢﻳﺪﻉﻗﻮﻝ
ﺍﻟﺰﻭﺭﻭﺍﻟﻌﻤﻞﺑﻪﻓﻠﻴﺲﻟﻠﻪ
ﺣﺎﺟﺔﻓﻲ ﺃﻥﻳﺪﻉﻃﻌﺎﻣﻪ
ﻭﺷﺮﺍﺑﻪ
Ya Allah ka hane mu daga fadar karya a koda yaushe. Ya Allah kasa mu kasance, daga cikin bayinka masu fadin gaskiya komai rintsi, komai wahala. Ya Allah ka hane mu, daga aikata miyagun ayyuka maras kyau. Ya Allah ka shiryar damu akan bin sunnar Annabin ka, Annabi Muhammad Sallahu Alaihi Wasallam ‪#‎ Ameen
‪TUNATARWA‬:-
Daga cikin mutanen da suka Zamani tareda Manzon Allah Annabi Muhammad S.a.w, rubuta muna sunan mutum daya tak Namiji ko Mace daka sani daga cikinsu?

.
.
.

.
.
.
.
.
.

.KA YI KOKARIN KASANCEWA NA DAYA KO NA BIYU KAWAI
Abu Kabshata al-Anmari ( RA) ya rawaito cewa Manzon Allah(saw) ya ce: `` Ita dai duniya ta jama`a hudu ce;
- Bawan da Allah ya azurta shi da dukiya da ilmi, yana jin tsoron Ubangijinsa a cikinsu, yana sadar da zumuncinsa a ciki, yana kiyaye hakkin Allah a ciki, to wannan shine a mafificin matsayi.
- Da kuma bawan da Allah ya azurta shi da ilmi, amma bai ba shi dukiya ba, sai ya zama yana da niyya ta gaskiya, inda yake cewa; da ace ina da dukiya, da na yi irin aikin wane (na farkon), to shima niyyarsa za ta yi aiki, su biyun ladansu daya.
- Sai kuma bawan da Allah ya azurta shi da dukiya, amma bai ba shi ilmi ba, yana ta fantamawa a dukiyar tasa ba tare da wani ilmi ba, ba ya tsoron ubangijinsa a ciki, ba ya sadar da zumuncinsa a ciki, ba ya kiyaye hakkin Allah a ciki, to wannan yana mafi munin matsayi.
- Sai kuma bawan da Allah bai ba shi dukiya ko ilmi ba, sannan yana cewa; da dai ace ina da dukiya, da na yi irin aikin wane (na ukun) a ciki, to shima yana da sakamakon niyyarsa, zunubinsu du daya ne (da na ukun).
Imam Ahmad da Tirmidhi ne suka rawaito shi.
IDAN KUNNE YA JI, JIKI YA TSIRA !!
.
.
.
.
.
.
.
.
.
ARE YOU ONLINE?
Daga cikin Masu Ruwaito Hadisai na Manzon Allah s.a.w, rubuta muna sunan guda daya tak daka sani.
Muje zuwa...
ABU HURAIRA (RA)


This page:
Help/FAQ | Terms | Imprint
Home People Pictures Videos Sites Blogs Chat
Top
.