pep.zone
Welcome, guest. You are not logged in.
Log in or join for free!
 
Stay logged in
Forgot login details?

Login
Stay logged in

For free!
Get started!

Mobile Blog


dadylasting.pep.zone

mafarki na............

16.09.2016 02:29 EDT
MAFARKI NA......!!! "..... Iska mai karfi gami da rugugin aradun da ake yi asararin samaniya, su sukayi sanadiyar watsewar abokanan firar tamu.. Kowa ya kama gabansa domin samun tseratar da kansa daga barazanar da hadarin nan kemana, akan daga yanzu zuwa kowanne lokaci zai iya zubar da ruwa...... Tsoki nayi gami da duba agogon hannuna," dukama dare bai yiba ashe 12 saura....." banji dadi ba, saboda bashi bane lokacin tashi daga firar tamu wadda zan iya kiranta ta gado....:" kawai kilama barazanace bana ruwan za,aibaa" nace cikin takaici,,, Mintuna biyar suka kawoni dan matsakaicin gidan mu,, har a lokacin rugugi hadarin nan keyi, idan kallonka yakai a fuskata kuma saika dauka tamkar wani tashin hankali ya sameni saboda tsananin murtikewarta,, hakan kuma ya samu daliline sakamakon korar kare da hadarin nan yai mana, domin harga allah banji dadi ba.......... Bude dan akurkin dakina nayi wanda yake like ajikin dan matsakaicin gidan namu,,,,,abin karin takaicin kakkarfar iskar nan tayi sanadiyar dauke dan hasken wutar lantarkin da muka samu a daren. Karfe 12 daidai haka agogondake daure a dan sirirn hannuna ta nuna na dare, adaidai lokacin kuma nakai kafaduna a saman wata yar dattijuwar katifata, har a lokacin raina bace yake,,,,,,domin idan akwai abu guda wanda na tsana arayuwata shine kwanciya da wuri,,,,, "Toh dame mutum ma zaiji talaucin ko zazzafan zafin da ake ko kuwa wanan jarababben kwaron mai nacin tsiya wato sauro???" Cikin takaici na fadi haka gami da juyawa...... "Yaro kudi da kake ganinsu sune gishirin wannan rayuwar da muke ciki,,,matukar akacema bakada su to bakai ba dandana roman wanan zamanin......" na tuno kalaman wani dattijo da muka hadu dashi wajan wata mai dan wake dakecan karshen layin mu..........!!! Yanzu da inada kudi tayaya zan kwanta cikin wannan akurkin dakin mai zafin tsiya gami da tarin sauro??....tayaya zan kwanta saman wannan rubabbiyar katifar??? tayaya....tayaya....tayayaya.. ......???" haka dai naita lissafe lissafan karya dana bogi tunda banda ko Ahu,,,har barci yazo yayi awon gaba dani,,,,,, To acikin barcinfa labarin mai ban al'ajabin ya samo asali........... A karkashin wata bishiya na ganni wadda ban iya gane ko wacce iri bace gatanan dai kamar mangwaro ita kuma ba yazawa ba,,,,,,nayi zugudum cikin takaici, na buga uban tagumi inata lissafin duniya amatsayina na wanda baida ko a nini,,,,yunwar cikina kadai ta isheni tashin hankali ballantana talaucin dake bibiyata arayuwa tamkar wnda ya zagi Dan'karuna.....duk da sanyayyiyar iskan dake kadawa amma ni gumi kawai nake tamkar wanda ya hadiyi kunama.... Kamar da wasa naji launin iskar ya canja,, cikin abnda bai wuce kyaftawar ido ba naji hancina ya shakoman wani daddadan kamshi wanda atake alokacin ban iya tantance kona miye......cikin sauri na dago kaina gami da kai kallona inda naji kamshin ya fito...... Gabana yayi wani mummunan faduwa,,zuciata ta harba jinin jikina da karfi cikin jijiyoyina,,,,,,idanuwana suka firfito nabi wajan da kallo baki bude, hatta tsigar jikina alokacin ta tashi...... Ta karaso gurina sannu a hankali cikin taku dai-dai,,, wata santaleliyar kyakkyawar budurwace wacce ban taba ganin irin taba a duniya duk da tsabagen kallon finafinan kasashen yamma da nike..... "Sannunka da hutawa" tace dani da daddadar kuma tattausar muryanta.. Har a lokacin kallonta nake tamkar idanuwana zasu zubo kasa..... "yayy.......yawwa san....nunki" Nace da ita muryata na rawa tamkar wanda yayi gamo da wani mummunan abin tsoro...... Zaunawa kusa dani tayi ba tare data nemi izinina ba, har a lokacin kallonta nake kyawunta kuma sai dada kara bayyanuwa yake.. "haba yan samari irin wannan kallo haka ko kyaftawa bakayi......toh kabi sannu kada miyau ya zubo" Tace dani da wannan sassanyar muryan tata,,,hakan yayi sanadiyar dauke kallona gareta gami da dukar da kaina.. "yawwa kokaifa,,,,,koso kake ka gano muninane ??" ta kara cewa dani tana murmushi..... "Aa kiyi hakuri ba manufta kenan ba" nace da ita batare dana kalleta baa "uhm aikoda zaka shekara kallona ba yadda za'ai ka gano munina,,,, sbd ni cikakkar kyakkyawace" tana fadin hakan cikin wani irin Salo mai daukar hankali gami da jan aji, amma kuma da murmushi afuskarta Dago kaina nayi na kalleta a karo na farko bayan zamanta kusa dani "kwarai kuwa ka kara kallona domin ka kara fahimtar kyawuna" ta kuma cewa dani "kwarai kuwa na sheda ranki ya dade" nace da ita nima da dan murmushin yake afuskata..... A haka muka dan gaisa sama sama cikin rashin sabo, danni shine karona na farko dana taba fira da wata mace tsawon rayuwata. Bare wannan kyakkyawar mai kamar ita tai kanta.......shuru muka danyi kafin ta bata shurun da cewar- "Dama nazo in tayaka firane amma idan munyi tsada ka biyani!" murmushin yake na karayi duk da ta kada man gaba,,,, danni da naji zancen kudi musamman idan ni zan bayar sai inji gabana ya fadi. "Hmmmm dayake kuma kinyi rashin sa'a ninan ko ahu banda shi,,,,sai dai idan yunwar cikina zan fiddo miki ki siya ki cire kudin firarki ki bani sauran" "Hahahaah "tayi daria "kanada ban daria wlh" tace dani batare da tabar dariyar ba " To ai kwanda in fadi maki domin ni ita kadai gareni" "Na sani"tace dani,,, Sannan ta karta da cewa "shiyasama na taho ma da tsaraba" tace dani gami da saka hannunta cikin wata jaka dake rataye akafadanta,,,wani abu na ga ta fiddo nannade da wata irin farar takarda mai kyalkyali "Amshi kaci"tace dani gami da mikomin,,,,ba musu na amsa gami da bude farar takardar,,,,,wani irin nau'in abincine wanda ni ban san sunansaba amma yafi kama da 'Cake' "kaci ba damuwa idanka yadda dani"tace gami da kallona,,,,,a wannan karon ma ban mata musuba kamar yadda bance komai ba kawai naci gaba daci.... ".........sai dana gama ci sannan ta kara mikomin wata yar doguwar roba duk da ban budaba nasan lemo ne ciki "Amshi kasha " amsa nai ban tsaya bata lokaci ba na bude gami da kaiwa baki.....kalllona taci gaba dayi gamida kuramin ido har a lokacin akwai murmushi afuskarta....... Safke robar nayi daga bakina gami da cewa; "ALHAMDULLAH!!!" "Yawwa haka yayi ko?" tace dani tana dai murmushin nan "Sosai kam dan sai yanzu naji na dawo mutum" "Hahahahahaa" tai daria "ka cika ban daria bari in tashi in baka guri" ta kara cewa dani gami da mikeawa.. Saurin dago kaina nayi na kalleta "haba ya zaki tafi ki barni ko tsayawa bakiyi muyi firaa?" nace da ita cikin damuwa kuma har cikin zuciana banso ta tafi ta barni "yanzu nan duk firar da mukai bata isheka ba?" tace dani tana kallona da fararen idanuwanta masu tsananin haske.. "kofa sunanki ban sani ba kuma baki gayamin daga inda kike ba???" "hmmmm kar ka damu idan mun hadu gobe na gaya maka!" "a ina zan ganki gobe????" "kai dai kada ka damu zamu hadu" tana gama fadin haka ta fara tafiya,,,,cikin sauri nima na mike nabi bayanta "ki tsaya kiji dan allah......karki tafi ki barni........ki tsaya dan alllah...." haka na biyota inatai mata mgn amma bata tsaya ba ni kuma na gaza komo ta............. . "said said said ........gam gam gam!!!" can cikin barci naji anata kiran sunana gami da bubbugamin kofar daki..... "kai ka tashi mana har gari ya waye ko sallah bakaiba" aka kara cewa dani,,,, dama nasan Tsohonane yake tayar dani....... Cikin takaici na yankewar mafarkina na tashi gami da bude idanuwana..... A cikin dan akurkin dakina dai nake, tamkar in fashe da kuka haka naji "ko ayaushe zan kara tozali da wannan kyakkyawar????. ...." da babanmu bai tayar dani ba nasan dana kamota ko sunnanta ta gayamin,,,,,, "Amma gskia Dad ya kwapsamin daya tsinkemin daddadan mafarkina wlh" cikin takaici na fadi haka gami da mikewa tsaye Ga mamakina sai naji cikina cike nida kuma nasan na kwant da yunwa.....sannan kuma sai naji dandanon lemon nan abakina.......nai tsaye sototo a tsakar dakina... "Wannan abu yapi kama da almara pa ......amma dai allah ya kaimu dare Inga zan kara haduwa da ita........!!! Toh ku mu hadu da daddaren!!!" Admin dadylasting whatsapp 08137963075 www.Facebook.com/dadylasting


This page:
Help/FAQ | Terms | Imprint
Home People Pictures Videos Sites Blogs Chat
Top
.