pep.zone
Welcome, guest. You are not logged in.
Log in or join for free!
 
Stay logged in
Forgot login details?

Login
Stay logged in

For free!
Get started!

Mobile Blog


dadylasting.pep.zone

BAKAR HARKALLA <>

03.01.2017 15:24 EST
collection by dadylasting
BAKANO DA KUDI....

Labarin Bakar Harkalla.
Bashir Lawal (Sir Gangara).

SHIMFIDA

Dauda mugun aiki, tunda nake bantaba ganin hatsabibin matashi kamar Dauda ba, babban masanine kwararre afannin ta'addanci da sanin hanyoyin aikata manyan laifuka, Dauda ya dade da lumewa kaf acikin aikata miyagun aiyuka wadanda tuni suka taimaka masa wajen cin lambar girmamawa atsakankanin matasa yan uwansa masu aikata manyan laifukan ta addanci, wanda tuni ya zama shugaba mai sarrafa akalar tsagerun da suka fado harkar bariki, shan miyagun kwayoyi, sata da fashi da makami, kisan gilla, safarar kwayoyin, damfara, da duk wani aiki daka iya ingizo keyar kudade Dauda kwararrene akansa. . Dauda dan asalin kwaryar birnin kanone, ya taso acikin fadala, awata unguwa da ake kira Tudun Qul-Qul, akaramar hukumar Dala, tun Dauda yana yaronsa aka fahimci halayensa bana kirki bane, domin shi indai harka bata kudi bace, baya ma shiga shirginta, mutum ne mai zalama wanda yayi ma kudi mugun sabo, ansha rabashi fada da matasa yan uwansa akan yana son sai ya cucesu idan suna raba kudi, atarihi babu wanda kudinsa suka taba fadawa hannun Dauda suka fita lafiya salin alin, batare da Dauda ya ha'inceshi ba, koda kuwa babansa ne ko babarsa. . Ance halin Dauda na zalama ya fito filine bayan ankaishi makarantar horar da tsagerun yara, awata unguwa da ake kira Hausawa acikin birnin kano, inda wata rana ya mamayi malaminsu ya faskamai duka da wani karfen ankwa dake hannunsa, saboda wani alhaji dake unguwar ya bada sadakar dubu uku yace asiyama su Dauda abinci, amma malamin yaki, ance Dauda ya tunamai yakai sau shida akan kudin amma malamin yayi buris dashi, wan nan yasa saida ya bari da safe za'afito dashi daga daki acikin mari don yayi sallar asuba, ya mamyi malamin dake kokarin kwancemai sarkar kafa, ya bugamai ankwar dake hannunsa nan take malamin ya fadi kasa sumamme, Dauda ya fige mabudin dake hannun malamin ya bude ankwar dake hannunsa, san nan ya lalube duk kudin dake aljihunsa, ya fita da sauri yabi daki daki ya kwance dukkan yan marin dake gidan tsagerun yaran, san nan ya tattara sarkokin da ankwar ya zuba a buhu ya sulale dasu. . Ance saida akayi aka kwana biyu malamin su Dauda bai farfado ba, saboda dukan da Dauda yayi mai ya tafa kwakwalwarsa, Dauda kuma tuni ya isa ga wani dan kwankwan mai sana'ar karafa ya siyarmai da dukkan sarkokin duka, san nan ya isa unguwarsu. . An sake ruwaitowa cewa Dauda a wunin ranar da ya gudo daga gidan tsagerun yara, da yammacin ranar ya lumama wani matashi wuka a wuya, saboda ya sayi gurasar hamsin ya bashi dubu daya yace ba canji, sai yar hayaniya tashiga tsakaninsu, nan take ya zare wuka ya sokeshi awuya, da daren ranar yan sanda suka zo nemansa gida, yana jin labari bai tsaya ko inaba sai tashar zuwa legas. . Watan Dauda 7 a legas ya shiga kungiyar yan fashi da makami, suka addabi agege da sata, a can ya samu lakabinsa na Dauda Mugun aiki, saboda alokaci daya ya zama jagora acikin tawagar yan fashin saboda rashin kirkinsa, ance ya taba lumama wata bayarebiya mai tsohon ciki,wuka a ciki ya farke cikin ya ciro yaron dake cikin shima ya farke mai ciki yace uwarka ta jama, karka rayu cikin talauci, tundaga lokacin suka samai suna Mugun aiki. . Ance su Dauda sun je gidan wani kanar din soja fashi, anan rana ta baci, aka kashe mutum biyar acikinsu, aka kame sauran ciki harda Dauda mugun aiki, Aranar da za'a kashe su suma alokacin ya samu taimakon wani soja tsohon dan daba, wanda yace sun rinka haduwa da Dauda adabar shaye shaye, shi ya kubutar da Dauda, san nan yace ya maza yabar garin legas in ba haka aka sake kamashi ba ruwansa. . Tundaga ranar Dauda ya dawo kano, ana saura sati daya zaben kasa na sherar 2011, ya fada cikin tawagar yan bangar siyasa sara suka, aka rinka daukarsu duk inda ake son atayar da hankali, bayan anci zabe, akayi musu alkawuran sama musu aikinyi, Dauda yana cikin wadanda guguwar siyasa ta tafi dasu izuwa shiga aikin Dan sanda. . FARKON LABARI Daudan da ake kallo amatsayin rikakken dan ta adda, masani aharkar kisa da neman kudi ta kowanne hanya, yanzu yana cikin rundunar yan sanda ta kasa amatsayin maikaci, ya kuke lallon rayuwar rikakken dan ta adda arundunar tsaro, . Yanzu labarin zai fara, BAKANO DA KUDI, Labarin wani dan sanda ne, Dauda Mugun aiki, wanda yake rikidewa da aikinsa na dan Sanda, yayi yunkurin tarwatsa birnin kano, yan rikata ta duka, tare da tayar da hankalin kowa, acikin bakar harkallarsa ta son tara kudi, da damfara, mutane da yawa suna rasa rayukansu, dayawa suna rasa dukiyoyinsu, wasuma muhallinsu suke rasawa, yan'uwa da yawa sun tarwatse saboda harkallar Dauda Mugun aiki.
FARKON LABARI
Dauda mugun aiki, ya isa hedkwatar yan sanda dake
bamfai, kai tsaye ofishin kwamishina ya nufa, don amsa
kiran sa, tun da asubar fari aka shaidamai cewa
Kwamishinan yansada na son ganinsa karfe 9 na safe,
har ya isa ofishin kwamishinan zuciyar sa ba adaidai
take ba, domin tunjiya bai iya bacci ba saboda wani
sabon tunani da yayi wuf ya makale azuciyarsa, dashi
ya kwana arai yanata bitarsa, tare da neman mafita
Dauda na iya tariyo abunda ya hanashi bacci adaren
jiya cikin abunda yayita bitarsa aransa .
Tabbas na dade a aikin dan sanda Dauda ya tabbatar
ma da kansa, kusan shekaru biyar kenan tundaga 2011
zuwa yau 2016, amma har zuwa yanzu ban ajiye wani
abu na naira dubu biyar ba, da wan nan aikin dan
sandan, akullum dakyar nake iya samun abunda nake
bukata, ga basuka sunyimin yawa, yanzu takaiga
ba'ama bani bashi, lallai inaga lokaci yayi da zan kara
futo da hanyoyin karama harkalla yawa yayi, don dan
cin hancin naira hamsin dari, bazai taba kaini ga inda
nadade ina mafarki ba,''
Dauda ya lalubi aljihun wandonsa sai acikin daren ya
tuna lallai fa bashi da ko kwabon da zai karyafa da
safe, kusan dukkan albashin da dauda yake samu
awajen shaye shaye da neman mata yake karewa,
kamin wata ya raba tuni Dauda ya fara tunanin wasu
hanyoyin samun kudi ta barauniyar hanya, kodai ya ba
da aron bindigarsa da ake bashi zuwa gadin gidan wani
attajiri agoron dutse, ga rundunar yan fashi insun dawo
su yaga mai nashi kason, ko kuma afara sintirin bagaira
ba dalili, ana zaluntar masu ababen hawa, amma duk
wan nan sam baya gamsar da zuciyar Dauda mugun
aiki, shi da yake son yayi kudi lokaci daya taya zai
tsaya yana bata lokaci akan wadan nan hanyoyi, ''dole
ne na fito da wasu hanyoyin samun kudi masu kauri
Dauda yasanar da kansa adaren jiya, wanda samun
hikimar tara kudi adare daya yasashi murmushin
mugunta bayan ya tabbatar da cewa zai iya tara kudi
masu yawa ta wan nan hanya daya gano acikin wan
nan dare.
Duk da iskancin Dauda da rashin da'a awajen aiki, baisa
kwakwalwar Dauda ta tashi a aikin banza ba, Dauda ya
kware awajen bincike mai zurfi, yasan makwantar mugu
amatsayinsa na babban mugu, kwakwalwarsa tana ja
indai aharkan bincikene, ya dade yana gano miyagun
laifuka da binciko manyan kesa kesai, saboda saninsa
da harkar, wan nan yasa dukda bashi da igiya ko daya,
bai hana kwamishina jansa jikiba yanasashi wasu
hamimman aiki don ya ga tunaninsa yana lissafi mai
kyau.
Wan nan yasa lokacin da Dauda ya isa ofishin
kwamishinan, sai ya ajiye wan nan tunanin gefe guda,
don yasan wan nan tunanin sirrinsa ne shi kadai baya
son kowa yajishi, ya tura kofar sannu ahankali ya shiga
ofishin ya tarar da kwamishina zaune akan kujerarsa
yana jiran zuwansa, tundaga nesa Dauda ya kamema
babban dan sandan san nan ya isa gaban teburin ya
bushe yana jiran umarni.
Kwamishinan ya kalleshi bayan ya dauke hannu akan
wasu takardu, yace yana kallon Dauda mugun aiki,
''Maza ka shirya yanzu, zan turaka karamar hukumar
Munjibir ne, don ka bincikomin wata rigimar fulani da
manoma, wadda ta balle adaren jiya domin rahoton da
D P O magaji ya turomin ban yarda dashiba, kaje ka
bincikamin da kanka, don na yarda da aikinka, sai ka
kula da ka gama ka dawo ina jiranka,''
Dauda ya dade da nitsa can cikin wata duniya daban,
sam kwamishina bata bakinsa yake kawai abanza,
domin Dauda sam baya gane me yake cewa, zuciyarsa
cike take makil da tunane tunane birjik, wadanda ya
fara adaren jiya, don haka ayanzu natsuwa kawai yake
bukata ta inda zai kebanci ya samu damar kara bitar
yanda shirinsa zai samu nasara, da yanda zai kaiga
ribar lissafinsa, da cikar mafarkinsa na samun
mahaukatan kudi acikin yan kwanaki kalilan kamar
yanda ya shirya.
Dauda ya fita ofishin kwamishina da sauri, bayan ya
amshi umarnin da tuni ya mance me akeso ya aikata
inyaje munjibir, dominshi abu uku kawai zai iya tuna
kwamishinan yafada acikin zantukan dayayi masa,
Fulani, manoma, munjibir, Dauda kaitsaye dakinsa ya
nufa dake makale ajerin rukunin dakunan yansanda
dake bamfai, ya fada kan gadonsa bayan ya kulle kofar
dakin dakyau, san nan yaci gaba da tariyo tunaninsa na
jiya,
Tun adaren jiya Dauda mugun aiki yay mafarkin ya
zama hamshaki attajiri wanda akano ake damawa dashi
ta kowanne fage, don haka ya farja da zimmar sai ya
cika wan nan mafarki nasa da dukkan dubarun daya
kwana yana bitarsu, akaron farko Dauda ya yanke bin
hanyar tayar da hankali sanya tsoro da firgita zukatan
al'umma da yawa amatsayin ramin farautarsa, ya
tabbatar da dole dubunnan rayuka su mutu, wasu
dubunna su tagayyara, jinane su zuba akasa, muddun
burinsa na tara abun duniya zai cika wan nan ba'abakin
komai yake ba awajensa.
Ya shirya aiki da kungiyoyin yan ta'adda, wadanda zasu
zama karnukan farautarsa aboye, ya shirya bacewa
acikin kakinsa na dan sanda, tare da kawo gaggarumin
hargitsi arundunarsu ta tsaro, batare da idanun duniya
sun farga da karamin kwaro mai tafka ta'asa na cikin
kanan yan sandan dake jaha ba.
Misalin karfe goma na safe, Dauda mugun aiki na
dakinsa akwance, yana nazarin rigima ta kaga da
yakamata ya ballo, da kara anziga wasu kudaden acikin
ma'ajiyarsa ta banki don ya lura kudaden da yake jiyan
shigarsu asusunsa ayanzu bazasu isheshi neman kayan
aikin tabar gaza ta gaba ba, ya sadaukar da kudinne ga
karnunakan farautarsa na farko don ya samu damar
kamasu atarko na gaba.
Kamar wanda aka tsirama allura a ido, cikin sauri
Dauda mugun aiki ya mike tsaye yana kallon sakon tex
din daya fado wayarsa ayanzu, wanda yake kunshe da
dan gajeren bayani kan cewa dubu dari sun fada
ma'ajiyarsa ta banki, daga wani suna da aka rubuta
Inusa bakin kare mai haushi, nan da nan Dauda ya fice
daga dakin ya nufi wani kangon ...


This page:
Help/FAQ | Terms | Imprint
Home People Pictures Videos Sites Blogs Chat
Top
.